Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bayyana cewa hukumar ta yi jigilar maniyyata 67,000 daga cikin 73,000 da suka rage daga kujerun da aka ware na jin dadin jama'a.
Kwamishinan hukumar a bangaren tsare-tsare da bincike, Sheikh Suleiman Momoh shi ya bayyana haka a ranar Talata 20 ga watan Yuni a Abuja. Legit ya wallafa.
Ya bai wa 'yan Najeriya tabbacin jigilar dukkan mahajjatan zuwa kasar Saudiyya kafin rufewa a ranar 24 ga watan Yuni, Daily Trust ta tattaro.
Hukumar ta ce maniyyata 6,000 ne kadai suka rage
Ya bayyana cewa yawan mutanen da aka yi Jigilarsu zuwa kasa mai tsarki ya nuna irin shirin da hukumar ta yi a bana idan aka kwatanta da shekarun baya.
Ya kara da cewa wannan shekarar ita ce ta farko da hukumar ta cike dukkan kijerunta da aka ware, inda ya ce har wadanda za su bi jiragen yawo ba za a bar su a baya ba.
Sheikh Suleiman ya shawarci maniyyata anan gaba da su bi tsarin ajiya na hukumar saboda kullum farashin kara sama ya ke yi, cewar Leadership.
A cewarsa:
"Wannan tsarin ya samu gindin zama a hukumar saboda rage radadin karin farashin kudaden hajji saboda yanayin tattalin arziki.
"A shekarar 2019 farashin bai wuce N1.5m, a 2022 ya kai har N2.5m, yanzu kuma N3m. Haka zai ci gaba da karuwa idan ba gwamnati ce ta kawo wani tsari ba.
"Mafi yawanci muna amfani da Dala ce, idan ta yi sama dole farashin zai karu, shi yasa muke ba da shawarar yin amfani da tsarin ajiya ta wannar hukumar."
Mafi yawan wadanda suka makalen suna daga cikin masu tafiya ta jiragen yawo ne.
An dauki hayan kamfanin Arik Air don jigilarsu zuwa kasar Saudiyya bayan samun matsalar.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com