Yanzu Yanzu: Ko da gaske ne Buhari ya bukaci Tinubu ya dakatar da binciken Emefiele da sauransu? gaskiya ta bayyana


Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi martani ga rahotannin cewa shi ya nemi kada shugaban kasa Bola Tinubu ya binciki yan majalisarsa. Legit Hausa ya wallafa
.

A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, Garba Shehu, tsohon kakakin tsohon shugaban kasar, ya yi watsi da rahoton cewa Buhari ya fada ma shugaban kasa Tinubu ya daina binciken da ke gudana na wasu yan majalisarsa.

Buhari bai nemi Tinubu ya dakatar da binciken yan majalisarsa ba, Garba Shehu

Shugaban kasa Tinubu da magabacinsa, Buhari sun yi ganawar sirri a birnin Landan, yayin ziyarar da shugaban kasar ya kai kasar Amurka a ranar Litinin, 26 ga watan Yuni.

Ya rubuta a shafin nasa:

"ABUN DA BUHARI BAI FADA MA SHUGABAN KASA TINUBU BA.

"Idan za a yarda da soshiyal midiya, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na neman kada magajinsa, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya binciki wasu tsoffin jami’an gwamnatinsa. Labarin kanzon kurege ne, kada mu tattauna shi ko ba shi karfi. Wannan labaran karya be, kuma bai fi haka ba. Abun godiya, babu wani mutum baya ga shugabannin biyu a dakin da suka gana, saboda haka babu wanda ke wajen da zai kwaso rahoton tattaunawarsu. Kamar yadda yake, tsohon shugaban kasar baya son yin katsalandar domin kada ya janye hankalin sabuwar gwamnati. Ya zabi komawa Daura yana fatan jin shirun da yake sowa kansa amma ya lura cewa ba haka abun yake ba, baki na ta tururuwa a safe, rana da dare, ya fice zuwa waje mai nisa. Burinsa ne neman a bari ya samu hutun da yake bukata, sannan kuma don gwamnatin Tinubu ta samu yanayin da ya dace don aiki da cimma alakawaran da suka dauka.”

Kalli wallafar a kasa:

Shugaba Tinubu ya sa labule da Buhari a Landan

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, a birnin Landan.

Yayin da ba a san takamaiman abun da suka tattauna a kai ba, wasu hadimai sun wallafa hotunan shugabannin biyu a soshiyal midiya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN