An daure dan Najeriya shekara 235 bayan ya danfari kasar Norway da jama'arta N525m ta intanet


Rahotanni daga Kudancin Najeriya na cewa sashen Kotun daukaka kara na Calabar, ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa wani fitaccen dan damfara na kasa da kasa mai suna Scales Olatunji, wanda wata babbar kotun tarayya ta same shi da laifin zamba ta yanar gizo da kuma karkatar da kudade da wata babbar kotun tarayya da ke zaune a Uyo, jihar Akwa Ibom ta yi a kan shari'ar.

Rahotun ya ce mai shari’a Agatha Okeke a ranar 27 ga watan Yuni, 2022 ta samu Olatunji da laifuka arba’in da biyar da suka hada da zamba ta intanet da almundahanar kudi da hukumar EFCC ta shiyyar Uyo ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 235 a gidan yari, ba tare da zabin tara ba. Jaridar PM News ta rahoto.

Ya danfari kasar Norway sukutun

 Hukumar EFCC ta gurfanar da wanda ake tuhumar ne a gaban kuliya, biyo bayan samun takardar koke daga ofishin ‘yan sandan birnin Oslo na kasar Norway, na neman taimakon hukumar EFCC wajen gudanar da bincike kan wasu ‘yan Najeriya da suka damfari wasu ‘yan kasar.

 Bincike ya nuna cewa wanda aka yankewa laifin na cikin gungun masu damfara ta intanet wadanda suka kware a Kasuwancin Email Compromise, watau BEC.

 Olatunji ya damfari gwamnatin Norway da ’yan kasar har zunzurutun kudi N525, 172, 580. Ya yi amfani da kudaden da aka samu wajen sayan kadarori na alfarma a yankunan da ke cikin jihar Legas.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN