Kalmomin da mata basu so

Ga tambayoyi biyar da bai kamata namiji ya rika yi wa mata ba, rahoton Premium Times.

1. "Yaushe za ki yi aure?"

Yan uwa maza, ba huruminka bane ka tambayi takwararka ko abokiyar aikina lokacin da za ta yi aure.

Mata na samun matsin lamba sosai daga al'umma da iyayensu da dangi kan aure, yi musu wannan tambayar na kara jefa su cikin damuwa.

Idan ya zama dole ka yi tambayar, ka tabbatar ka yi cikin yanayin da ya dace na mutuntaka da raha.

2. "Kina kara kiba."

Yin tsokaci kan kibar mace batu ne da ya kamata ka kame bakinka daga furtawa don muna zamani wanda ake danganta kyau da yanayin jikin mace.

Don haka, fada wa mace cewa ta yi kiba 'tamkar fada mata cewa bata cikin wadanda ake yi wa kallon suna da kyau' ne. Hakan na iya shafar kimarta a matsayin mace, ta rika ganin tamkar bata cika 'ya mace ba.

Don haka, duk yadda mace ta ke, ko mai kiba, ko siririya, ka guje yin magana kan jikinta. A yi wani hiran daban.

Idan kuma ita ta taso da batun, ka san yadda za ka yi dabara ka isar da sakonka cikin hikima.

3. "Shekarun ki nawa?"

Idan dai kai ba likita bane ko jami'in yin rajista, ka guji yi wa mace wannan tambayar, musamman idan haduwarku ta farko ne.

Mata da dama ba su son a san shekarunsu, don haka yin wannan tambayar bai cika yi musu dadi ba.

4. "Ba ki da hankali."

Babu wanda ke son a kira shi mara hankali, don haka ka guji kiran matarka ko budurwa ko abikayar aiki mara hankali musamman kokacin da aka samu sabani.

Idan abu ya shiga tsakanin ka da mace kuma ka na ganin 'tana kambama abin fiye da kima' ka daure ka kwantar da zuciyarka kada ka fada mata bakar magana, don wasu na da riko a zuci sosai.

5. "Kina da juna biyu ne?."

Ina rokon ka a matsayin saurayi dan Najeriya ka guji yin wannan tambayar da mata, idan ba matar ka bane. Tambaya ce wanda ba ta yi wa mata dadi kuma ba hurumin ka bane

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN