Marigayi Dr Khadi Zubairu Malami, ya rasu ne a safiyar ranar Litinin, 5 ga watan Yuni bayan yar gajeruwar rashin lafiya a gidansa da ke Birnin Kebbi, jaridar Leadership ta rahoto.
Rahotanni sun kawo cewa Zubairu ya mutu ya bar matar aure daya da yara biyar kuma tuni aka binne shi daidai da koyarwar addinin Musulunci a Birnin Kebbi. Legit ya wallafa.
Gwamna Nasir Idris Gwandu, wanda ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa gidan marigayin ya yi ta'aziyyar ga Malami da iyalan mamacin sannan ya roki Allah SWT ya yafe masa kurakuransa a nan duniya da lahira, jaridar The Sun ta rahoto.
Manyan masu fada aji da dama daga cikin jihar Kebbi da wajenta sun yi tururuwa zuwa gidan margayin domin yi wa tsohon AGF din da iyalan mamacin gaisuwan ta'aziyya.
BY isyaku.com