Matar Shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta shiga ofis, ta fara aiki a matsayin First Lady


Uwar gidan shugaban ƙasa "First Lady," Sanata Oluremi Tinubu, ta shiga ofishinta domin fara aiki a matsayin mace lamba ɗaya a Najeriya ranar Litinin, 5 ga watan Yuni
.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Misis Tinubu ta isa bangaren matar shugaban ƙasa bisa rakiyar masu tsaronta a Villa da ke birnin tarayya Abuja. Legit ya wallafa.

Daga zuwanta, ta samu kyakkyawar tarba daga babban Sakataren fadar shugaban ƙasa, Mista Tijjani Umar, da shugabannin ɓangarorin sashin matar shugaban ƙasa.

Wane aiki matar shugaba Tinubu ta fara yi a ranar farko?

Daga nan, matar shugaban ƙasa ta fara tafiya rangadi domin duba ofishin da ke ɓangarenta, wanda ya haɗa da ofishin shugabanci, ICT, shirye-shirye, midiya da kuma ofishin tsara ayyuka.

An haifi Oluremi Tinubu a ranar 21 ga watan Satumba, 1960, mahaifiyarta yar kabilar Itsekiri ce yayin da mahaifinta ya kasance bayerabe.

Ta yi aiki a matsayin matar gwamnan jihar Legas tsakanin 1999 zuwa 2007, daga nan kuma ta lashe zaɓen Sanata mai wakiltar Legas ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya.

Sanata Oluremi Tinubu ta shiga harkokin taimako da ba da tallafi da dama da nufin sanya walwala da jin daɗi a fuskokin mutane masu ƙaramin karfi a mazaɓarta.

Ta taɓa haɗa gasar karanto haruffan kalma da aka fi sani da, "Spelling Bee competition," a tsakanin daliban sakandiren jihar Legas wanda ya samar da gwamnan rana ɗaya a zangon mulkin mijinta.

Mai gidanta, Bola Ahmed Tinubu, ya samu nasarar lashe zaben shugaban ƙasa wanda ya gudana a watan Fabrairu kuma aka rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN