Gwamnan Kwara ya rage ranakun aikin ma'aikata zuwa kwana 3 marmakin 5


Gwamnatin jihar Kwara ta amince da daukar matakin rage radadi na wucin gadi domin kawo sauki ga ma’aikata biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.

 Shugabar ma’aikata ta jihar, Mrs Susan Modupe Oluwole, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai, Murtala Atoyebi ya fitar. PM News ya rahoto.

 Oluwole ya lura cewa Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya bayar da umarnin rage kwanakin aiki daga kwanaki biyar zuwa uku a mako ga kowane ma'aikaci.

 Ta kuma umurci dukkan shugabannin ma’aikatu da hukumomi (MDAs) na jihar da su gaggauta tsara tsarin da ke nuni da sauya ranakun aiki ga kowane ma’aikaci da ke karkashin su.

 Sai dai shugabar ma’aikatan ta gargadi ma’aikatan da kada su ci mutuncin gwamnan, inda ta jaddada cewa za a kara sanya ido kan ayyukan MDA a ofishinta domin tabbatar da bin doka da oda.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN