Mukaddashin Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), Olukayode Adeolu Egbetokun, ya yi Allah-wadai da lamarin da ya tayar da hankulan jama’a inda tawagar ‘yan sanda suka bi ta kan wani dan Najeriya da mota a ranar Alhamis 29 ga watan Yuni, 2023 a Ekpoma, jihar Edo.
Ya umurnin cewa a kawo yan sandan da ke tsare a jihar Edo hedikwatar rundunar ta Abuja a ranar Litinin domin ci gaba da daukar mataki. Jaridar The Nation to rahoto.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a ranar Juma’a ya ce:
“An yi kira ga jama’a musamman mutanen Ekpoma da su kwantar da hankalinsu domin shugabancin NPF mai ci ba zai lamunci irin wannan aiki na rashin da’a da saba doka ba. ".
Published by isyaku.com