Shugaban yan ta'adda Digo Gudali ya mutu bayan ya bi ta kan wata nakiya da yaransa Yan ta'adda suka binne a jihar Zamfara.
Wata majiyar soji a yankin Arewa maso Yamma, wacce ta tabbatar wa PRNigeria faruwar lamarin, ta ce ‘yan ta’adda ne suka dasa bam din don kawar da sojojin Operation Hadarin Daji, wadanda ke aikin share fage a bakin dajin Gando a karamar hukumar Bukkuyum ta jihar.
Majiyar ta ce "Bam din an nufi sojoji ne, amma ya tashi da wuri ya kashe shugaban 'yan fashi Dogo Gudali, da wasu mayakansa."
“Dogo Gudali da ‘yan kungiyar sa suna ta addabar Anka, Gummi, Bukkuyum, da wasu sassan jihohin Sokoto da Kebbi.”
Published by isyaku.com