Yanzu haka dai rundunar ‘yan sandan Abuja na ci gaba da bin diddigin wani mutum da ake zargin ya tsere da wata mota kirar Mercedes Benz GLB 250.
Wani dillalin mota mai suna Manga, ya shigar da kara yana zargin wani Henry da ke ikirarin yana zaune a Gwarinpa, ya bace da daya daga cikin motocinsa.
Abokin Manga wanda shi ma ke cinikin motoci, ya ɗauki Benz mai daraja N55m da nisan maaunin gudu 19000 zuwa ga Henry don yin tuƙin gwaji. ’Yan mintuna kaɗan a cikin motar gwajin, abokin Manga ya ba da uzuri don cire kuɗi daga wani mai PoS. A wannan lokacin ne Henry ya bace da motar.
Published by isyaku.com