Yan bindiga sun sako mata 3 daga cikin mutanen da suka sace a jihar Neja

Some women kidnapped by bandits in niger state

Yan bindiga sun sako mutane uku daga cikin mazauna garin Kafin Koro da wasu al’ummomin da suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Paikoro a jihar N Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

 Idan ba a manta ba, a watan da ya gabata ne ‘yan bindiga suka abkawa al’ummar garin tare da yin garkuwa da mutane sama da 50.

 An tattaro cewa tun farko wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun sami ‘yanci bayan sun biya kudade daban-daban a matsayin kudin fansa, yayin da sauran kuma ke hannun su.

 Wani dan unguwar Umar Farouq Akike, ya tabbatar da sakin matan uku a wani sako da ya wallafa a Facebook a ranar Talata, 6 ga watan Yuni, 2023.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN