Shugaba Bola Tinubu yana ganawarsa ta farko da Gwamnonin Jihohi 36 na Tarayya da aka fi sani da Nigeria Governors’Forum (NGF) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
An fara taron ne da misalin karfe 12:36 na rana. Jaridar The Nation ta rahoto.
Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamnonin Zamfara, Kano, Taraba, Kogi, Ogun, Nasarawa, Bayelsa, Adamawa, Ebonyi, Lagos, Rivers, Osun, Jigawa, Benue, Taraba, Delta, Enugu, Rivers, Oyo, Plateau. Kebbi, Abia, Imo, Bauchi
Mataimakan gwamnonin Edo da Nijar ne ke wakiltar jihohinsu.
Wadanda ba a gansu ba kafin fara taron sun hada da gwamnonin Katsina, Kaduna, Gombe, Borno, Cross River, Akwa Ibom, Anambra, Ekiti, Ondo da Sokoto.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima; Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume.
Shugaba Tinubu ya gana da gwamnonin jam’iyyar sa ta APC mai mulki da aka fi sani da Progressive Governors’ Forum (PGF), a ranar Juma’ar da ta gabata.
BY isyaku.com