Tinubu ya yi kus-kus a wayar tarho da Shugaban Majalisar Turai: Abin da suka tattauna

Nigeria President Bola Ahmed Tinubu on phone call with EU President

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi kira ga Tarayyar Turai da su taimaka wa Najeriya da Afirka wajen karfafa tsaro da ci gaban tattalin arziki don kawar da talauci a nahiyar.

 Shugaban ya yi magana ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban majalisar Turai, Mista Charles Michel a ranar Laraba. PM News ta rahoto.

 Majalisar Turai ita ce cibiyar EU wacce ke bayyana alkiblar siyasa gabaÉ—aya da fifikon Tarayyar Turai.

 A cewar Tinubu, Najeriya da ma nahiyar Afirka baki daya za su bukaci taimako da hadin gwiwar kawayenta da abokan zamanta na ci gaba kamar kungiyar EU domin magance tsananin talauci a nahiyar.

 Ya bukaci kungiyar EU da ta duba takamaiman yankunan da ke fuskantar kalubalen tsaro kamar tafkin Chadi da yankunan bakin teku.

 Tinubu ya yi alkawarin ci gaba da tuntubar kungiyar Tarayyar Turai da sauran kasashe mambobin kungiyar.

 Ya ce talauci da rashin tsaro su ne abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba don haka zai yi duk abin da ake bukata don magance su.

 Shugaban Majalisar ya yi amfani da damar tattaunawar ta wayar tarho inda ya sake taya Tinubu murnar zabensa.

 Ya kuma yi alkawarin karfafa hadin kai da hadin gwiwa da Najeriya bisa mutunta juna da moriyar juna.

 Michel ya yi nuni da cewa Najeriya na da muhimmanci ga kungiyar EU da kasashen duniya, yayin da ya bukaci shugaban Najeriya da ya ci gaba da hada kai da kungiyar ta EU a dukkan bangarorin da suka dace.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN