Wasu da ake zargin yan yahoo ne sun yi wa wata kaka da ke zaune a unguwar Urban a karamar hukumar Sapele ta jihar Delta fyade.
Rahotanni sun bayyana cewa, wadanda ake zargin ‘yan damfara ne sun shiga gidan matar da sanyin safiyar 16 ga watan Yuni, inda suka yi mata fyade, wanda hakan ya sa ta zubar da jini sosai a al’aurarta.
Tuni dai aka garzaya da wadda aka tsohuwar zuwa asibiti inda a halin yanzu take jinya.
Mazauna yankin sun ce ya zama ruwan dare ga irin wadannan yara maza na aikata miyagun laifuka.
An yi imanin cewa wannan wata sabuwar hanya ce a gare su ta aiwatar da ayyukan bukatun tsibbu don samun kuÉ—i.
Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar ba ta mayar da martani kan wannan lamari ba.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com