Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ayyana Alhaji Bello Matawalle a cikin wadanda ta ke nema.
Rahoto ya fito daga Tribune cewa EFCC ta na farautar Bello Muhammad Matawalle bisa zargin rashin gaskiya da ya tafka a lokacin ya na ofis.
Bello Muhammad Matawalle ya yi gwamna na shekaru hudud aga 2019 zuwa 2023 a Zamfara. Wani babban jami’in hukumar ya shaidawa Sunday Tribune cewa a ranar Asaba, EFCC ta bukaci DSS ta bada umarnin cafke Bello Matawalle.
Zuwa yanzu ba mu samu cikakken bayanin laifuffukan da ake tuhumar Matawalle da aikatawa ba.
EFCC ta na so jami’an hukumar DSS su bada dama a damke tsohon Gwamnan a duk inda aka gan shi a fadin Najeriya domin ayi bincike a kan shi.
Hakan ya na zuwa ne ‘yan kwanaki kadan bayan shugaban Najeriya ya dakatar da Abdulrasheed Bawa daga kujerar da yake kai na shugaban EFCC.
Kafin a dakatar da Abdulrasheed Bawa, ya fito fili ya na musayar kalamai da tsohon Gwamnan wanda ya bukaci a dakatar da shi daga bakin aiki.
EFCC Statement
— EFCC Nigeria (@officialEFCC) June 18, 2023
EFCC Has Not Declared Matawalle Wanted
The attention of the Economic and Financial Crimes Commission, EFCC, has been drawn to a report, entitled, Alleged N70b Fraud: EFCC Declares Ex-Zamfara Gov, Matawalle Wanted, which appeared in the Sunday Tribune of June 18,… pic.twitter.com/PDxoPpEEA5
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com