Wani mutum mai suna Utobong, ya mutu a cikin dakinsa da ke Osina Street Mile 2 Diobu a Fatakwal, Jihar Ribas. Shafin isyaku.com ya samo.
Dan jaridar Rivers, Allwell Ene, wanda ya bayyana hakan a wani sakon Facebook a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuni, 2023, ya ce marigayin na tare da wata mace a lokacin da lamarin ya faru.
A cewarsa, an samu fakitin tramadol guda biyu, da na inganta jima'i, da kwalabe 2 na abubuwan sha na makamashi black bullet a gefen gawar.
“Al’amarin ya faru ne a dakinsa inda aka ce ya kwana da wata mace. Matar ta gudu daga dakin lokacin da aka tsinci gawar. An samu wasu abubuwan sha guda biyu, fakitin tramadol guda biyu da kuma wani maganin kara kuzari a gefensa a cewar majiyar,” Mista Allwell ya rubuta.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com