Yadda mai gidan haya ya gayyato ‘yan fashi suka kashe dan haya, suka yi wa yayansa mata 2 fyade

Yadda mai gidan haya ya gayyato ‘yan fashi suka kashe dan haya, suka yi wa yayansa mata 2 fyade

 
Yadda mai gidan haya ya gayyato ‘yan fashi suka kashe dan haya, suka yi wa yayansa mata 2 fyade

Adebayo Salami, wani magidanci ne a jihar Oyo, a halin yanzu yana hannun ‘yan sanda bisa zarginsa da gayyatar ‘yan fashi da suka kashe daya daga cikin masu haya tare da yi wa ‘ya’yansa biyu fyade.

 A cewar Adewale Osifeso, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, an kama wanda ake zargin ne da sanyin safiyar Juma’a. Daily trust ta rahoto.

 Osifeso ya ce a lokacin da ake yi masa tambayoyi, Salami ya amsa cewa ya gayyaci kungiyar Yan fashin ne domin yin fashin a yankin Apaatuku, inda aka kashe Ogedengbe tare da yi wa ‘ya’yansa mata guda biyu fyade.

 Ya kara da cewa an mayar da binciken zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) domin gudanar da bincike.

 Kakakin ‘yan sandan ya ce an kama Ibrahim Rasaq, Abiodun Olalekan da kuma wani Abolade Morenikeji da laifin fashi da makami, an gano cewa gungun ne da suka kai farmaki Apaatuku/Onireke.

 “A ranar 14 ga Mayu, 2023 da misalin karfe 4 na safe, wasu ’yan fashi da makami sun kai farmaki Apaatuku/Onireke a Akobo, Ibadan, inda suka yi wa mazauna garin fashi da makami.  Maharan sun kashe wani dan haya mai suna Makanjuola Ogedengbe tare da yiwa ‘ya’yansa mata guda biyu masu shekaru 14 da shekara 10 fyade, a lokacin da lamarin ya faru.

 “An mayar da shari’ar zuwa sashin binciken manyan laifuka, Iyaganku, domin gudanar da bincike mai zurfi.  A yayin bincike, an gano cewa wani Ibrahim Rasaq mai shekaru 31;  Abiodun Olalekan, 32;  da Abolade Morenikeji, mai shekaru 34, wadanda tun da farko an kama su da laifin yin fashi da makami a rukunin gidajen Sawia da ke Ogbere a Ibadan, wanda aka ruwaito a ranar 16 ga Afrilu, 2023, su ne ‘yan kungiyar da suka kai farmaki a unguwar Apaatuku/Onireke.

 “’Ya’yan mamacin biyu, Morenikeji da Sodiq su ne suka yi masu fyade.  Sodiq, wanda ake zargin shugaban kungiyar ne, an kashe shi ne a farmakin da jami’an tsaron yankin suka kai.  Maharan sun kuma harbe wani mai gadin dare, wanda a halin yanzu yake samun kulawa.

 “A ranar 16 ga watan Yuni, 2023, da misalin karfe 3:30 na safe, an kama wani Adebayo Salami, wanda babba ne a kungiyar kuma mai gida a Ajara Olohunda, Akobo a Ibadan a kan lamarin.

 “A yayin da ake yi masa tambayoyi, ya amsa cewa ya gayyaci kungiyar ne domin yin fashin a yankin Apaatuku, inda aka kashe Ogedengbe tare da yi wa ‘ya’yansa mata guda biyu fyade.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN