Tsagerun Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Babban Malamin Addinin Musulunci


Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da da babban limamin masallacin Uso da ke karamar hukumar Akure ta arewa a jihar Ondo, Alhaji Ibrahim Bodunde Oyinlade.

An tattaro cewa yan bindigar da yawansu ya kai biyar sun sace malamin addinin mai shekaru 67 a gonarsa. Legit ya wallafa.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an sace malamin ne da misalin karfe 3:00pm a ranar Asabar, 17 ga watan Yuni a Asolo Farm Camp, da ke garin Uso.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun bude kafar zantawa da yan uwan malamin da abun ya ritsa da shi.

Maharan sun tuntubi dangin malamin
Majiyar ta fada ma manema labarai cewa basu riga sun bukaci kudin fansa ba amma dai sun sanar da yan uwanda da su nemo "kudi mai kyau" domin ceto malamin.

Majiya ta ce:

"Sun tuntubi iyalin jim kadan bayan sun yi garkuwa da shi, suna masu sanar da iyalin cewa yana tare da su amma basu riga sun bukaci kudin fansa ba."

Ya kara da cewar an kai rahoton lamarin zuwa ofishin yan sandan Uso.

A halin da ake ciki, an tattaro cewa an fara taron addu'o'i na musamman a masallacin da ke garin domin neman Allah ya dawo da malamin lafiya.

Rundunar yan sanda ta yi martani
Da take martani, kakakin rundunar yan sandan jihar, Misis Funmilayo Odunlami sannan ta ce jami'an rundunar da yan sa kai suna a daji suna neman malamibn, jaridar Punch ta rahoto.

Ta ce:

"Da misalin karfe 6:00pm na yau (Asabar), an kai wani rahoto hedkwatar Uso, cewa babban limamin Uso ya je gonarsa da safe sannan kuma bai dawo ba, daga bisani mutanensa suka bi gonar, sun ga waya da motarsa amma ba su ga mutumin ba, DPO da jami'ansa da yan sa kai suna daji a yanzu haka don gano inda mutumin yake."

By/Daga - Click/Latsa isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN