A halin yanzu dai wasu dalibai na gudanar da zanga-zanga a Gusau babban birnin jihar Zamfara kan sace wasu abokan karatunsu guda biyar.
Masu zanga-zangar wadanda akasari daliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau ne, sun tare babbar hanyar Zariya zuwa Sokoto, inda masu ababen hawa da fasinjoji suka makale. Daily trust ta rahoto.
Wasu daga cikin rasinjoji sun yi kokarin ganin daliban sun bude hanya don su wuce, amma daliban sun tsaya tsayin daka.
Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da ‘yan fashin suka addabi jama'a .
A ranar Litinin din da ta gabata, wasu ‘yan bindiga sun kashe wani likita tare da yin garkuwa da mutane 10, ciki har da iyalan likitan da aka kashe a wani hari da suka kai a kauyen Jangebe da ke karamar hukumar Talata Mafara.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun afkawa al’ummar ne da misalin karfe 1 na dare inda suka fara harbe-harbe daga bangarori da dama.
An yi garkuwa da al’ummar Jangebe da yawa. Daga watan Janairu zuwa yau, an sami akalla hare-hare hudu na mamayewar 'yan bindiga a cikin al'umma a cewar mazauna garin.
A watan Fabrairun 2021, an sace 'yan mata fiye da 200 daga makarantar sakandare a cikin al'umma.
A watan Disamba 2022, an yi garkuwa da dangin dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Talata Mafara a cikin al'umma.
A harin na ranar Litinin, miyagun sun fasa katangar gidan likitan don samun shiga. Rahotanni sun ce sun harbe shi ne nan take suka tilasta wa kansu shiga cikin gidan suka tafi da ‘yan uwansa da wasu mazauna unguwar. Sun kuma kona wata motar soji a kusa da gidan mamacin.
Sa'o'i 24 bayan harin, Gwamna Dauda Lawal ya bukaci 'yan majalisar dokokin jihar Zamfara da su hada kai da bangaren zartarwa domin ceto jihar daga rugujewar shekaru da dama.
“Zamfara na fuskantar manyan kalubale da suka hada da rashin tsaro zuwa rugujewa a harkar ilimi, da dai sauran muhimman batutuwan da ke damun su,” Lawal ya shaidawa ‘yan majalisar wakilai ta 7 bayan kaddamar da ta a ranar Talata.
An dai yi amfani da kokari daban-daban wajen magance tabarbarewar tsaro a jihar, da suka hada da katse hanyoyin sadarwa da hana ‘yan bindiga shiga garuruwa, amma matsalar ta ci gaba.
BY isyaku.com
Innalillahi Allah yakawo sauki
ReplyDelete