Yadda kalaman Gwamna Nasir Idris suka gaskata rahotun isyaku.com kan rawar da Abubakar Malami ya taka don zamansa Gwamna

Tsohon babba Lauya, Kuma Ministan Sharia Tsohon Ministan Sharia kuma babban Lauyan Gwamnan tarayya Abubakar Malami SAN, ya ziyarci Gwamnan jihar Kebbi Dr Nasir Idris a gidan Gwamnati da ke Birnin kebbi ranar Lahadi 4 ga watan Mayu 2023.  Abubakar Malami wanda ya sami tarbon Gwamna Nasir ya gaya wa jama'a a gidan Gwamnati cewa Abubakar Malami ne tushen nassarar siyasasa har ya zama Gwamnan jihar Kebbi.

Tsohon babba Lauya, Kuma Ministan Sharia Tsohon Ministan Sharia kuma babban Lauyan Gwamnan tarayya Abubakar Malami SAN, ya ziyarci Gwamnan jihar Kebbi Dr Nasir Idris a gidan Gwamnati da ke Birnin kebbi ranar Lahadi 4 ga watan Mayu 2023.

Abubakar Malami wanda ya sami tarbon Gwamna Nasir ya gaya wa jama'a a gidan Gwamnati cewa Abubakar Malami ne tushen nassarar siyasasa har ya zama Gwamnan jihar Kebbi.

Kalaman Gwamna Nasir Idris a yau, sun tabbatar da rahotun shafin labarai na isyaku.com na ranar 17 ga watan Afrilu, wanda ya bayyana irin rawa da Abubakar Malami ya taka wajen ganin nassarar Nasir Idris ya zama Gwamnan jihar Kebbi. (Latsa nan ka karanta Labarin)

A wata takarda da Mai taimaka wa Gwamna kan harkar watsa labarai Yahaya Sarki ya fitar, kuma aka raba wa manema labarai a birnin Kebbi ranar Lahadi. Ya ce Gwamna Nasir ya ce:

"Ministan ya kasance wanda ya taka rawar gani tun shigowar Gwamna cikin harkokin siyasa, tsayawar takararsa a matsayin dan takarar Gwamna, nasara a zabe da hawansa mulki.

 Dakta Nasir Idris ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar tsohon Ministan Shari’a da ya ziyarce shi a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi a ranar Lahadin nan.

 Gwamnan ya ce, duk da cewa wasu mutane ba sa son ya fadi hakan a bainar jama’a, amma a matsayinsa na malami, zai ci gaba da fadin gaskiya, yana mai godiya ga Abubakar Malami sosai kan yadda ya taimaka masa wajen samun nasara a harkokin siyasarsa.

 Dakta Nasir Idris ya bayyana farin cikinsa da yadda tsohon ministan shari’a ya cika wa’adin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba shi, duk da kasancewarsa matashin da ya taba rike irin wannan matsayi a tarihin Najeriya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN