Yadda kan kungiyar kwadago ya rabu bayan Tinubu ya cire tallafin man fetur


Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta hadu da gagarumin cikas a shirinta na shiga yajin aiki a ranar Laraba, 7 ga watan Yuni. Legit ya wallafa.

A cewar jaridar This Day, alamu sun nuna cewa kawunan kungiyar sun rabu gabannin ranar da aka tsayar don fara yajin aiki yayin da kungiyar NLC reshen arewa da kudu maso yamma suka janye daga daukar wannan mataki.

Ci gaban na zuwa ne bayan Bayo Onanuga, daya daga cikin kakakin jam'iyyun All Progressives Congress (APC), ya zargi shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, da kokarin hargitsa kasar da sabuwar gwamnati yayin da yake yi wa jam'iyyar Labour Party aiki.

Dalilin da yasa yajin aikin da NLC ta shirya kan cire tallafin mai da Tinubu ya yi ba zai yi karfi ba

An tattaro a daren Asabar, 3 ga watan Yuni cewa an siyasantar da yajin aikin da NLC ke shirin zuwa kan cire tallafin man fetur da gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta yi, yayin da rassan kungiyar na kudu maso yamma da arewa maso yamma suka yanke shawarar janyewa daga zanga-zanga

Sai dai kuma, domin ganin yajin aikin ya yi tasiri, shugaban NLC na kasa ya rubuta akalla kungiyoyi 43 wasika don su shiga yajin aikin da aka riga aka shirya yi, rahoton Punch.

Wasu daga cikin kungiyoyin da NLC ta rubutawa takarda sun hada da kungiyar malaman Najeriya (NUT), kungiyar malaman jami'a (ASUU), Kungiyar ma'aikatan shari'an Najeriya (JUSUN), kungiyar ASUN, Kungiyar NANNM da sauransu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN