Type Here to Get Search Results !

Wane rawa ne Abubakar Malami ya taka wajen ganin Nasir Idris ya ci zaben Gwamnan Kebbi a jam'iyar APC ?


Bayan da hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Kebbi ta sanar da Dr. Nasir Idris a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan jihar Kebbi bayan kammala karashen zabuka da aka yi ranar 15 ga watan Afrilu.

Jita-jita ya kaure tsakanin al'ummar jihar Kebbi dangane da yadda ta faru har Nasir Idris ya zama zababben Gwamnan jihar Kebbi. A bisa lissafi da mahangar tafiyar siyasar jam'iyar APC a jihar Kebbi.

Akwai mabanbantan tsokaci, ra'ayi, da zarge-zarge daga jama'a na yiwuwar wani shiri na boye kafin Nasir ya sami albarkar ubannin siyasar jihar Kebbi a jam'iyar APC. Babu abbaci kan wannan zagin.

Tun farko dai, Nasir Idris ya fito neman takarar kujerar Dan Majalisar tarayya ne Mai wakiltar kananan hukumomi guda uku da suka hada da Birnin kebbi, Kalgo da Bunza. Wanda su ne matakin karfinsa na siyasa bisa rabin kansa a waccan lokaci.f

Bayan tasowar wasu lamurra da ba a yi zato ba lokacin lissafin da ubannin siyasar APC na jihar Kebbi suka yi. Sai dai bayan da kura ta lafa sakamakon hazon lamurran bazata da suka bulla, kwatsam sai aka tsayar da Nasir Idris a matsayin Dan takarar kujerar Gwamnan Kebbi a jam'iyar APC.

Bisa ga dukkan alamu Nasir bai shirya wa fuskantar wannan kalubale ba, amma lokaci daya ya tsinci kansa a wannan mataki. 

Tun farko dai Ministan Sharia, kuma babban Lauyan Gwamnatin Tarayya Dr. Abubakar Malami SAN, ya bayar da gudunmuwar motocin alfarma ga tawagar Dan takarar APC Nasir Idris. Da wadannan motoci ne Nasir ya yi hidimar kampen.

Kazalika wasu hadimai da masu taimaka wa Abubakar Malami a siyasarsa suka koma bayan Nasir domin taimaka masa.

A ranar zaben shugaban kasa, da Sanatoci ranar 18 ga watan Maris. Dan takarar jam'iyar APC na Sanatan Kebbi ta tsakiya kuma Gwamnan jihar Kebbi da ke kan kujerarsa ta Gwamna ya sha kasa a hannun Dan takarar jam'iyar PDP Adamu Aliero. 

An yi zargin cewa dalili da ya sa wannan karon Nasir Idris na jam'iyar APC ya lashe zaben Gwamna shi ne Abubakar Malami ne ya taimaka wa Nasir ya zama Gwamna saboda ababen alhairi da ya shuka a jihar Kebbi kafin wannan lokaci tare da yin aiki tukuru a jam'iyyance lokacin zabe kafin APC ta kai ga nassarar samun Dr. Nasir Idris a matsayin zababben Gwamnan jihar Kebbi. 

Sai dai duk gaba daya Allah ne ke bayar da sa'a da mulki, kuma da yardarsa ne kadai lamurra ke kasancewa.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN