Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta fara aikin ceto wasu sarakunan gargajiya biyu da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar.
LIB ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun sace Hakimin kauyen Balma da ke karamar hukumar Ningi, Alh Hussaini Saleh tare da kashe wani dan kasuwa Haruna Dan OC, ranar Lahadi, 11 ga watan Yuni, 2023.
A daren ranar Asabar 10 ga watan Yuni kuma wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Mai Anguwan Bakutunbe dake karamar hukumar Ningi, inda suka yi awon gaba da sarkin gargajiya, Idris Mai Unguwa da wani mai suna Ya’u Gandu Maliya.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Wakil, ya ce jami’an rundunar sun dukufa wajen ganin an sako wadanda lamarin ya shafa a lokacin da ya dace.
“Yanzu haka, ‘yan sanda a sashin Ningi suna ta kokarin ganin yadda za su kubutar da mutanen kauyen biyu da aka sace da ransu,” in ji PPRO.
“’Yan bindigar da ake zargin ne suka yi harbe-harbe, suka tafi da hakimin kauyen, Alh Hussaini Saleh, mai shekaru 48 a duniya, zuwa inda ba a sani ba. Sannan kuma an sace hakimin kauye na biyu
“Yan bindigar sun harbe wani Haruna Jibrin a kai. A lokacin da ‘yan sandan suka samu wannan kiran, an tura tawagar ‘yan sanda zuwa wurin, inda suka ceto wanda abin ya shafa, suka garzaya da shi babban asibitin, inda Ningi ke jinya. Daga baya wani likita ya tabbatar da mutuwarsa."
Da yake bayyana yadda aka yi garkuwa da mutanen, shugaban riko na karamar hukumar Ningi, Ibrahim Zubairu, ya ce sarkin Balma na zaune da jama’a a fadarsa da ke Balma lokacin da ‘yan bindigar kimanin 3 suka zo fadar sa kafin su tafi da shi.
A cewarsa, Alhaji Haruna, yana kan babur dinsa yana komawa gida, sai ‘yan bindigar suka bindige shi har sau biyu.
BY isyaku.com