Rundunar ‘yan sandan Edo ta kama wani yaro dan shekara 16 da laifin lalata wata yarinya ‘yar shekara 2.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Edo, Chidi Nwabuzor, wanda ya tabbatar da kama shi, ya ce wanda ake zargin ya aikata laifin ne a unguwar Egba da ke karamar hukumar Uhunwonde a ranar 7 ga watan Yuni.
Sashin kula da jinsi na sashen binciken laifuka na gudanar da bincike kan lamarin. Nwabuzor ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike.
Da ‘yan jarida suka yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya ce;
“Yarinyar ‘yar shekara biyu takan zo wajen kanwata. Ta zo a wannan rana, sai na ce mata ta koma gida cewa kanwata ba ta gida amma ta ki tafiya.
“Don haka, sai na É—auke ta, na kwantar da ita a kan gadon. Amma ban Æ™azantar da ita ba. Ban shige ta ba, sai kawai na sanya al'aurata a tsakanin cinyarta.
"Ban san abin da ya same ni ba saboda ban taba yin haka a baya ba."
BY isyaku.com