Jami'an Protokol sun kasance a Majalisar tun da karfe 6 na safe don shirya kujerun manyan mutane da baƙi. Jaridar The Nation to rahoto.
Sai dai a lokacin da ‘yan barandan suka isa wurin, sai suka karbi kujerun da aka ware wa kafafen yada labarai, iyalai da kuma matan sabbin ‘yan majalisar da kuma baki da aka gayyata.
Kokarin da ’yan Protokol suka yi na adana kujerun ya sa ‘yan barandan sun yi musu bulala inda suka yayyage tufafinsu tare da raunata su.
Daya daga cikin ma'aikatan Protokol Victor ya sami raunuka a idanunsa, hannayensa da fuskarsa tare da yayyage tufafinsa.
BY isyaku.com