Gwamnan jihar Kebbi Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu ya amince da nadin Dakta Shehu Nuhu Koko na karamar hukumar Koko Besse a matsayin sabon Sakatare na dindindin.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikata na jihar Kebbi, Alhaji Safiyanu Garba Bena wanda aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Litinin. Mai taimaka wa Gwamnan Kebbi kan harkar watsa labarai Yahaya Sarki ya sanar da haka a takarda da ya fitar.
An kuma tura sabon wanda aka nada zuwa ma'aikatar lafiya.
A cewar sanarwar, Gwamna Idris ya kuma amince da nadin mukaman sakatarorin dindindin a jihar.
Wadanda lamarin ya shafa sun hada da Muhammad Sani Umar Ma’aikatar Kananan Hukumomi, Garba Umar Dutsinmare, Ma’aikatar Kudi, Aisha Usman, Ma’aikatar Kasafin Kudi, Zaki Dahiru, Al’amuran Gwamnati, Aliyu Mustapha Gwandu, Gidan Gwamnatin Kebbi, Joel Aiki, Ma’aikatar Gona da Kabiru Aliyu, SAN, ma’aikatar shari’a.
Sauran sun hada da: Aishatu M. Maikurata, Ministry of Women, Ahmad Yarima, Ministry of Business , Kudirat Shuaibu Diri , Ministry of Environment, da kuma Ibrahim Umar, Ma'aikatar Albarkatun Ruwa.
Sauran sun hada da Mustapha Abubakar Tata, Sashen Harkokin Protocol, Suleiman Sani Augie, General Administration, Saidu Buhari Warah, Ma’aikatar Yada Labarai, Aliyu Labaran, Sashen Ayyuka na Musamman da Abubakar Ahmed, Ma’aikatar Filaye.
Takarda ta ce wannan sauyin ya fara aiki nan take kuma mikawa da karbar ragamar shugabanci na ma'aikatu wajibi ne a gudanar da shi ranar, ko kafin ranar 14 ga watan Yuni.
BY isyaku.com
Ayukan ku su na sweet. Sannun ku
ReplyDelete