Sakamakon shawarar da majalisar dokokin jihar ta ba Gwamna Alia na dakatar da shugabannin kananan hukumomi 23 domin bayar da damar gudanar da bincike a harkokin kudadensu, hukumar kula da harkokin kananan hukumomi da sarauta (BLGCA) a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni, ta umurci ciyamomin da su mika mulki ga manyan jami'ai a hukumominsu. Legit Hausa ya wallafa.
Shugabannin kananan hukumomi 23 sun nunawa Gwamna Alia na Benue yatsa
Sai dai da suke martanin gaggawa a wani taron manema labarai a ranar Asabar, shugabannin kananan hukumomin sun bayyana cewa ba za su ba umurnin yan majalisar ko na hukumar BLGCA hadin kai ba.
Mike Uba, shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi na Najeriya (ALGON), reshen jihar Benue wanda ya yi magana a madadin takwarorinsa, ya ce ba za su mika kai ga rashin ka'ida domin yin hakan zai zama illa ga jihar.
Ya ce zabarsu aka yi a kan kujerarsu tare da kansilolinsu a ranar 30 ga watan Afrilun 2022 na tsawon shekaru biyu wanda zai kare a ranar 30 ga watan Afrilun 2024.
"Har yanzu ku dakatattu ne", Gwamnan Benue ya yi martani ga fusatattun shugabannin kananan hukumomi
Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya ce har yanzu shugabannin kananan hukumomi 23 na jihar Benue dakatattu ne har sai an kammala bincike a kansu.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga ikirarin shugabannin kananan hukumomin a taron manema labarai a Makurdi, babban birnin jihar a ranar Asabar, 24 ga watan Yuni, rahoton Daily Trust.
Majalisar Dokokin Jihar Benue Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomi 23
Legit.ng ta kawo a baya cewa majalisar dokokin jihar Benue ta bayar da shawarar dakatar da shugabannin kananan hukumomi 23 a jihar a ranar Laraba, 21 ga watan Yuni kan zargin karkatar da kudade.
Kakakin majalisar, Aondona Dajoh, ne ya sanar da shawarar a yayin zaman majalisar bayan ya duba rahoton kwamitin wucin gadi da aka kafa domin binciken rahoton kudaden shiga da kudaden da aka kashe wanda gwamnan ya gabatar masa.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com