![]() |
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya magantu kan dakatarwar da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) da ya yi.
A jawabinsa na ranar Juma’a, 23 ga watan Yuni, yayin wani taron tattaunawa da ‘yan Najeriya mazauna kasar Faransa da makwaftan kasashen Turai, a gefen taron sabuwar yarjejeniyar hada-hadar kudade ta duniya da aka yi a babban birnin kasar Faransa, Paris.
Shugaban ya ce tsarin kudi na kasa karkashin Emefiele ya lalace. Ya kara da cewa ‘yan Najeriya da dama a kasashen waje ba sa iya aika kudi ga ‘yan uwansu saboda yawan kudin canjin da ake samu, inda ya ce yanzu ya zama tarihi.
“Tsarin kudi ya lalace. Mutane kadan ne ke yin jakunkuna na kudinmu sannan kai da kanka ka daina aika kudi gida ga iyayenmu talakawa. Window da yawa… amma wannan ya tafi yanzu, ya tafi. Mutumin yana hannun hukuma, ana yin wani abu a kan hakan, za su daidaita kansu.” Yace
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com