Da duminsa: An kama wata mata ta sace jariri dan kwana daya da haihuwa a asibiti

Da duminsa: An kama wata mata ta sace jariri dan kwana daya da haihuwa a asibiti

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas a ranar Juma’a ta kama wata mata ‘yar shekara 49 a kan zargin satar wani jariri dan kwana daya da haihuwa a asibiti.

 Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ranar Asabar.

 NAN ta wallafa cewa Hundeyin ya ce rundunar ‘yan sanda ta Ojokoro ce ta gudanar da kamen a ranar Juma’a bayan da ta samu rahoton aikata laifin da misalin karfe 6.00 na yamma.

 Ya ce rundunar ‘yan sanda ta samu labarin cewa wanda ake zargin ta isa asibitin ne (an sakaya sunanta) da sunan mara lafiya ne kuma aka ce ta sace jaririn.

 ” Ta shiga dakin mata ta dauki wani yaro dan kwana daya da haihuwa, yayin da mahaifiyar ta yi barci mai nauyi bayan an yi mata tiyata.

 “Wani majiyyaci ya lura da saurin motsin wanda ake zargin da jaririn a hannunta, ya sanar da hukumar asibitin kuma an kama wanda ake zargin.

 “Da aka yi mata tambayoyi, an gano cewa wanda ake zargin ta fito ne daga jihar Oyo.

 “Wanda ake zargin ta amsa cewa wani Alfa ne ya ba ta kwangilar samun jaririyar domin a yi amfani da shi wajen tsafin yin kudi,” in ji ta.

 Hundeyin ya ce binciken da aka yi ya nuna cewa wannan shi ne karo na biyu na satar yara da wanda ake zargin ta aikata.

 Ya ce an mayar wa mahaifiyar jaririn.

 Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin bayan an kammala bincike.

By/Daga - Click/Latsa isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN