Wani malamin cocin St. Martins Parish Mbape da ke Adikpo deanery a karamar hukumar Kwande a jihar Benue, ya tsere sakamakon mutuwar wata budurwa da ake zargin masoyinsa ce. Shafin isyaku.com ya samo.
An gano malamin cocin
mai suna Oliver Vershima da misalin karfe 7 na yamma a yammacin Lahadi, 4 ga Yuni, 2023, yayin da yake kokarin jefar da gawar matar.
Da yake magana da manema labarai a ranar Talata, wani dan asalin yankin, Terhemba, ya ce wanda ake zargin wanda aka tura aiki a shiyyar St. Augustine, Jov Mbahura, ya boye gawar matar ne a cikin dakinsa bayan ta mutu a lokacin da yake yunkurin zubar mata cikin gaba da fatiha.
"Lokacin da aka tambaye shi, an gano cewa shi (Oliver) ya yi wa matar ciki kuma sun yi ƙoƙari su zubar da cikin amma a cikin haka, matar ta rasa ranta da sanyin safiyar ranar," in ji shi.
Daga nan sai malamin cocin ya boye gawar a cikin dakinsa har dare ya yi domin ya dauke gawar daga kauyen ya gudu.
Terhemba ya kara da cewa "Abin takaici a gare shi, an gan shi ne a lokacin da yake kokarin fitar da gawar daga kauyen ."
Terhemba ya ce har yanzu ba a gano ko waye matar ba, inda ya kara da cewa ta fito ne daga wata unguwa da ke makwabtaka da garin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Catherine Anene, wadda ta tabbatar wa da jaridar Punch faruwar lamarin, ta ce an gano gawar matar tare da ajiye ta a dakin ajiyar gawa na Asibitin.
“Gawar yarinyar da aka ce ta ziyarci masoyin nata, an tsinto gawar kuma aka kai ta dakin ajiyar gawarwaki bayan da aka samu rahoto amma har yanzu ba a ga Oliver ba yayin da ya fito da gawar daga dakinsa ya gudu. ”
PPRO ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike.
BY isyaku.com