Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kori daya daga cikin jami’anta, Sgt. Ekpo Shimuyere, wanda ke aiki da sashin Sogunle bisa laifin kwace N98,000 daga wani matashi.
Da yake bayyana hakan ga manema labarai, kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya ce tuni ma’aikatan Provost ta ‘yan sandan ta tube Sajan din.
A cewar sa, Sajan ya karbi wayar saurayin ya kuma yi amfani da wani ma’aikacin POS wajen tura N98,000 daga cikin N100,000 da ke asusun bankin matashin. Hundeyin ya ce matakin da dan sandan ya dauka ya saba wa ka’idar aikin.
“’Yan sanda sun samu korafi daga wajen saurayin kuma jami’in ya musanta aikata laifin lokacin da aka tuntube shi. Sakamakon haka aka tsare shi domin kada ya yi ta’ammali da hujjoji. Mun rubuta wa bankinsa kuma muka sami takardar shaida. Mun sami damar gano kuÉ—in zuwa ma’aikacin POS, daga bisani ya tura kudin zuwa asusun jami’in Dan sandan. Mun bi tsari don samun bayanan asusunsa. An gayyaci wanda aka zalunta yayin gudanar da bincike, kuma ya bayar da shaida. An kuma gayyaci ma’aikacin POS, kuma ya ce jami’in ya bukace shi da ya tura kudin daga asusun matashin zuwa wani,” in ji Hundeyin.
Ya kara da cewa sajan din ya fuskanci shari'ar Orderly Room watau Kotun cikin gida na dokokin aikin Yan sanda.
“Kwamishanan ‘yan sanda na jihar Legas, Mista Idowu Owohunwa ya amince da korar jami’in Dan sandan mai lambar aiki 461654 da ke aiki da rundunar ‘yan sanda ta Sogunle.
Hundeyin ya ce kwamishinan ya gargadi jami’ai kan duk wani nau’i na cin hanci da rashawa, yana mai jaddada cewa korar da aka yi wa Sgt. Ekpo Shimuyere ya zama izna ga wasu.
BY isyaku.com