Dan fari ya kashe dan autansu mai shekara 4 da duka, ya datse kansa gida biyu

Cutar farfadiya

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wani matashi dan shekara 24 mai suna Amos Christopher bisa zarginsa da lakada wa kaninsa duka har lahira. Shafin isyaku.com ya samo.

 Wanda ake zargin wanda aka ce yana fama da ciwon farfadiya, ana zargin ya kashe dan su na karshe, Thyson Christopher mai shekaru 4, daga bisani kuma ya fille kansa a ranar Litinin, 19 ga watan Yuni.

 A cewar rundunar ‘yan sandan, wanda ake zargin wanda shi ne na farko a gidansu, ya yanke jiki ya fadi a ranar 18 ga watan Yuni, inda makwabta suka dauko shi suka dawo da shi gida.  

An ba da rahoton cewa yanayin lafiyarsa ya tabarbare tare da sauya halayensa da safe sa’ad da ya far wa mahaifiyarsa da kannensa da ke gida tare da shi da ƙarfi. 

An ruwaito cewa ya kama yaron dan shekara 4 ya ja shi zuwa cikin daki inda ya kulle kofar ya yi masa duka har lahira.  

Duk kokarin ceto yaron da mahaifiyarsa ta yi ya ci tura.  A halin da yake ciki na tashin hankali, an yi zargin ya kai gawar waje inda ya yi amfani da fartanya da ke hannunsa wajen datse kan yaron tare da fasa ta gida biyu.

 A yayin da Kakakin Rundunar SP Suleiman Yahaya Nguroje ke yi masa tambayoyi, wanda ake zargin da kyar ya yi magana ya ce bai yi komai ba, kuma kanin nasa yana gida.

 Da yake amsa tambayoyi, mahaifin wadanda ake zargi da kuma wanda aka kashe, Christopher Haruna, ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da yake gona, ya kuma tabbatar da cewa Amos na fama da farfadiya.

By/Daga - Click/Latsa isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN