Kwamitin majalisar wakilai kan harkokin sufurin jiragen sama ya umurci ma’aikatar sufurin jiragen sama ta tarayya da abokan huldarta a cikin shirin na Najeriya Air da su dakatar da ayyukan jirage da duk wani mataki dangane da kamfanonin jiragen sama.
Kudurin ya zo ne a yayin wani zaman bincike yayin da babban sakataren ma’aikatar da sauran masu ruwa da tsaki suka bayyana a gaban kwamitin. The Nation ya rahoto.
A wani kudiri na kwamitin wanda shugaban kwamitin, Nmolim Nnaji ya karanta, kwamitin ya ce an boye sirrin tsarin.
Kwamitin ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya kafa wani babban kwamitin shugaban kasa domin gudanar da bitar cikakken tsarin tafiyar da aikin jiragen saman Najeriya baki daya tare da baiwa gwamnati shawara kan hanyar da za a bi.
Har ila yau, ta bukaci duk daidaikun mutane, ko kungiyoyi, da ke da hannu a cikin rikicin da ake tafkawa mai suna "Nigeria Air tashi da saukar jiragen sama, an gurfanar da su gaban kuliya da kuma hukunta su.
Wani bangare na kudurin yana cewa:
“Binciken da aka yi a tsanake yana nuni da cewa atisayen na da matukar rufa-rufa, da kuma iya yin izgili da bata sunan Najeriya a idanun kasashen Duniya. Muna so mu rubuta cewa, kwamitin da ma majalisar dokokin kasar ba su da wata rawar da za ta taka wajen harkar jirgin Najeriya Air ko wani abu mai alaka da shi."
BY isyaku.com