Ta bayyana a karshe: Dalili da manyan Fastoci suka goyi bayan Peter Obi


Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana dalilin Bishop David Oyedepo, fasto Paul Enenche, da sauran fastoci na goyon bayan Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasa.

Ayodele ya ce bai kamata ƴan Najeriya su ga laifin fastocin ba ko su kira su na bogi, saboda abinda suke so kawai shi ne a samu a sauyi a ƙasar nan. Legit ya wallafa.

A cewar rahoton Nigerian Tribune, babban faston ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ta hannun kakakinsa, Osho Oluwatosin.

Ayodele ya bayyana fastocin basu bayar da wani wahayi ba amma sun yi furuci da addu'a domin nuna goyon bayansu ga Peter Obi.

Faston ya bayyana cewa kamata ya yi a ga laifin ƴan takarar jam'iyyun adawa saboda ƙin yin amfani huɗubar da aka yi musu domin su lashe zaɓen.

A kalamansa:

"Yakamata mutane su daina caccakar manyan fastocin da suka goyi bayan Peter Obi ya zama shugaban ƙasa. Bai kamata ku ga laifinsu ba saboda abinda kawai suke so shi ne canji."

"Wahala ta yi yawa a ƙasa sannan suna buƙatar canji. Basu bayar da wani wahayi ba, abinda kawai suka yi shi ne maganganu. Irin su Paul Enenche, Oyedepo, da sauransu basu bayar da wani wahayi ba domin Peter Obi."

"Abin dariya ne idan wani ya ce fastocin Najeriya sun ba shi kunya saboda ko waÉ—anda suka yi magana akan Æ´an takarar adawa ba wanda ya saurare su."

"Na bayyana cewa Tinubu ya shirya yin nasara ko ta halin ƙaƙa sannan na gayawa Obi da Atiku abinda yakamata su yi su ci zaɓen, amma sun yi hakan? Meyasa kuke ganin laifin fastocin Najeriya."

Oyedepo, Enenche sun bambanta da fastocin da suka ce ba za ayi rantsuwa ba

Ayodele ya yi ƙarin haske kan cewa fastocin da ya lissafo sun bambanta da sauran fastocin da suka ce ba za a gudanar da rantsuwa ba a ranar Litinin, 29 ga watan Mayun 2023.

"Bana magana ne akan fastocin da suka ce ba za ayi rantsuwa ba, ina magana ne akan waɗanda suka marawa Obi baya a lokacin zaɓe ta hanyar amfani da cocinsu." A cewarsa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN