Wani mutum mai shekaru 39 da haihuwa da aka kama da laifin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 7 a jihar Adamawa ya dora laifin da ya aikata a kan giyar Burukutu.
Wanda ake zargin, Sadiq Ahmed, da ke kan titin Abuja a karamar hukumar Yola ta Kudu a jihar ya amsa laifin lalata karamar yarinya a ranar Litinin, 12 ga watan Yuni, 2023.
Yayin da ake yi masa tambayoyi a hedikwatar ‘yan sanda a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, wanda ake zargin ya ce ya aikata laifin ne a lokacin da ya bugu da Burukutu.
Ya ce bai dauki komai ba sai Burukutu kuma ya yi nadamar lalata yarinyar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan korafin da mahaifin yainya ya kai.
Mahaifin ya sanar da ‘yan sanda cewa wanda ake zargin ya zo gidan sa ne a lokacin da ba su nan ya ba ‘yar sa kudi naira 10 sannan ya lalata ta.
PPRO ta ce kwamishinan ‘yan sandan, Afolabi Babatola, wanda ya nuna damuwarsa kan lamarin, ya sha alwashin tabbatar da gurfanar da wanda ake zargin a gaban Kotu.
BY isyaku.com