Gwamnatin tarayya karkashin jagoranci shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ta ce tana aiki ba dare ba rana domin ganin an fara bai wa ɗaliban Najeriya bashin kuɗi a watan Satumba da Oktoba, 2023.
Babban Sakataren ma'aikatar ilimi, David Adejo, ne ya sanar da haka ranar Laraba yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida a birnin tarayya Abuja. Legit ya wallafa.
Idan baku manta ba, shugaba Tinubu ya rattaɓa hannu kan kudirin bai wa ɗaliban Najeriya rancen da babu kuɗin ruwa ranar Litinin da ta gabata, kamar yadda The Cable ta tattaro.
Ƙarin bayani na nan tafe...
BY isyaku.com