Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya bayar da umarnin dakatar da shi biyo bayan wasu zarge-zargen cin zarafi na ofis. PM News ya rahoto.
A cikin wata sanarwa da ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya fitar, shugaban ya ba da umarnin dakatar da Bawa don ba da damar gudanar da bincike mai kyau a kan yadda ya ke aiki a lokacin da yake kan mulki.
Akwai manyan zarge-zarge da dama a kan sa na cin hanci da rashawa, ciki har da zargin da tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya yi.
Ya yi ikirarin cewa Bawa ya bukaci dala miliyan 2 daga gare shi kuma ya sa mutumin a kaset.
Akwai kuma zarge-zarge masu tsanani na cin zarafin ofishin da aka yi masa.
Willie Bassey, Daraktan Yada Labarai ya ce an umurci Bawa da ya gaggauta mika ayyukan ofishinsa ga Daraktan Ayyuka a Hukumar.
Daraktan zai kula da harkokin ofishin shugaban hukumar har sai an kammala bincike.
BY isyaku.com