Kwastoma Ya Sace Wa 'Yar Gidan Magajiya N92,300 Bayan Sun Gama 'Harka' A Abuja

J

ami'an ‘yan sanda a sun gurfanar da wani dan kasuwa mai suna King Dauda a gaban kotun yankin Kado da ke birnin tarayya Abuja. Legit ya wallafa.

Ana zargin King Dauda ne da ke unguwar Life Camp a birnin Abuja da satar makudan kudade har N92,300 na budurwarsa.

Daily Nigerian ta tattaro cewa wanda ake zargin ya musanta laifin da ake tuhumarsa akai.

Mai gabatar da kara, Stanley Nwafoaku ya fada wa kotu cewa a ranar 26 ga watan Mayu da misalin karfe 9:05 na safe, Bolaji Olufumi ta kawo kara a ofishin ‘yan sanda na Life Camp.

Yadda abin ya faru, kamar yadda mai gabatar da kara ya fada
Mista Nwafoaku ya ce a ranar 20 ga watan, wanda ake zargin ya gayyaci wadda take karar gidansa, bayan sun kwana tare sai ya sace mata jakar kudinta karama da ke dauke da kudi N92,300.

Ya ce duk kokarin da ta yi don gano inda jakar take da kuma kudaden nata daga Dauda abin yaci tura.

Ya kara da cewa aikata hakan laifine a dokar kasa da ya sabawa sashe na 288 na kundin tsarin mulki a kasa.

Lauyan wanda ake karar ya nemi alfarmar beli
Lauyan wanda ake zargi, Charity Nwosu ya nemi alfarmar beli inda ya yi amfani da sashe na 36 na kundin tsarin mulki da kuma sashe na 158 na dokar aikata laifuka.

Nwosu ya tabbatar wa da kotu cewa wanda ake zargin ba zai saba ka’idojin beli ba idan aka ba shi.

Mai shari’a, Muhammad Wakili ya tabbatar da ba da belin akan kudi N100,000 da kuma wanda zai dauki belin nasa.

Wakili ya ce mai daukan belin dole zai kawo shaidar lambar banki ta BVN da kananan hotuna guda biyu da katin shaida aiki wanda sai kotun ta tabbatar da ingancinsa.

Mai shari’a, Muhammad Wakili ya dage sauraran karar har zuwa 15 ga watan Yuni don ci gaba da sauraran karar, cewar rahotanni.

Kotun na zargin Oni Muyiwa da yi wa matarsa barazanar zai kashe ta a lokuta da dama idan sun samu sabani.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN