Kasar Sweden ta amince a ƙona Alƙur'ani a gaban Masallaci ranar Sallah


Rundunar ƴan sandan Sweden ta bada izinin gudanar da taron ƙona Alƙur’ani a gaban wani masallaci dake Stockholm babban birnin ƙasar  ranar Sallah Babba.

Jerin zanga-zangar adawa da Musulunci da kuma tarrukan  ƙona Alƙur’ani da ake yi a Sweden sun jawo saɓani tsakaninsu ga Turkiyya, inda ta tara mata hanyar shiga ƙungiyar ƙawance ta NATO. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

A baya bayan nan dai ƴan sandan Sweden sun ƙi bada izinin shirya taron ƙona Alƙur’ani, amma kotunan ƙasar sun ce hakan ya saɓa da haƙƙin faɗin albarkacin baki.

Wani ɗan gudun hijirar Iraƙi mai fafutukar haramta karanta Alƙur’ani a Sweden, Salwan Momika ne ya shirya taron.

A watan Janairun bana dai Turkiyya ta dakatar da tattaunawa da Sweden game da ƙudirinta na shiga ƙungiyar NATO bayan da shugaban jam’iyyar ƴan ra’ayin riƙau ta Denmark, Rasmus Paludan ya ƙona Alƙur’ani a kusa da ofishin jakadancin Turkiyya dake Stockholm.

Haka kuma ƙasashen Musulmi da dama irin su Saudiyya, Jordan, da Kuwait sun yi tur da ƙona Alƙur’anin da aka yi a watan Janairun.

A ranar Laraban nan dai Firaministan Sweden, Ulf Kristersson ya ce har yanzu ƙasarsa na fatan shiga NATO kafin taronta na watan gobe amma ba ya jin hakan za ta samu.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN