Da duminsa: Yadda Gwamnan PDP ya yi cacar baki da dan siyasa kan wajen zama a sahu ya fusata ya fice ya ki yin Sallar idi a Masallacin


Wasu bayanai da suka fito daga jihar Osun da safiyar ranar Sallar Layya na cewa Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya fice daga Masallacin idi  a fusace Osogbo , bayan da suka yi arangama da tsohon kakakin majalisar dattawa, Ajibola Basiru kan wajen zama.

 Wakilin Jaridar The Nation ya lura da yadda Basiru ya iso Masallacin tare da basarake Asiwaju na Osogbo Cif Tunde Badmus da wasu fitattun ‘ya’yan garin Osogbo domin gudanar da sallar.

 Basiru ya zauna a gurin da aka tanada a sahun gaba, amma daya daga cikin jami’an Protokol na Adeleke ya tunkari tsohon dan majalisar.

 Wakilin Jaridar The Nation ya lura da cewa Basiru ya koma wani sahu a layin gaba amma jami’in Protokol ya kalubalanci haka. 

.Bayan 'yan mintoci kaÉ—an Gwamna Adeleke ya isa filin Sallar Idi, sai Cif Badmus ya bar.wajen da yake zaune a sahu don tarbar Gwamnan daga bakin kofar shigowa Masallacin idi..

 Lokacin da ya dawo  sai aka lura jami’in protokol ya dage cewa ya kamata Basiru ya bar sahun gaba amma wasu ‘yan asalin garin suka bijire, suna masu cewa Basiru na daya daga cikin fitattun ‘ya’yansu.

 Lamarin ya haifar da hayaniya, wanda hakan ya sa Gwamna Adeleke ya koma motarsa ya zauna.  Bayan wasu mintuna ya sake dawowa ya lura Basiru na zaune a layin sahun gaba.  Sakamakon haka ya fita a fusace ba tare da ya yi sallah ba.

 Jim kadan da tafiyar Gwamnan sai jami’an ‘yan sanda suka rufe kofar shiga Masallacin idi, inda suka shaida wa masu ibada cewa suna da umarnin a kamo Basiru.

Masu ibada suka bijire, suka bude kofar.  Basiru da wasu jiga-jigan 'yan asalin garin Osogbo sun gudanar da Sallar Idi da addu'o'in a Masallacin.

Kokarin jin martani daga Basiru da mai magana da yawun Adeleke, Olawale Rasheed ya ci tura.

 Ba su amsa kira ko sakon text ba zuwa lokacin rubuta wannan rahoto.

Asali: Jaridar The Nation

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN