An kama wani dan majalisar dattawa na jabu, Ifechukwu Tom Makwe bisa zarginsa da laifin zamba ta yanar gizo €5.7million (N4,731,000,000).
Jami’an EFCC sun kama Makwe ne a unguwar Guzape da ke Abuja, biyo bayan wasu sahihan bayanan sirri kan ayyukan damfarar sa ta intanet.
Mai magana da yawun EFCC Wilson Uwujaren ya bayyana cewa da kama shi, an gano cewa wanda ake zargin mai suna da yawa (Fahad Makwe, Sanata Tompolo, Tom Makwe, Dr. Bran), ya damfari wani dan kasar Sipaniya Yuro miliyan biyar, da dubu dari bakwai (€5.7million). .
Makwe ya yi ikirarin cewa shi ma’aikaci ne na Hukumar Bincike ta Tarayya ta Amurka, wakilin FBI kuma lauyan diflomasiyya, kuma ya yi nasarar damfarar wanda ya cuta ta hanyar amfani da bayanan karya.
Wanda ake zargin dai ya fara damfarar matar ne tun a shekarar 2013 lokacin da ya fara haduwa da ita a shafukan sada zumunta.
Wilson ya tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com