Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya yiwa mukaddashin kwanturolan hukumar kwastam, Adewale Bashir Adeniyi ado a fadar shugaban kasa dake Abuja. Jaridar The Nation ta rahoto.
A ranar Litinin din da ta gabata ne Shugaba Bola Tinubu ya nada Adeniyi a matsayin mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam tare da wasu sabbin shugabannin tsaro da aka nada.
Kawata Adeniyi ya zo ne kwanaki kadan bayan mataimakin shugaban kasa Shettima ya yiwa mukaddashin sufeto-janar na ‘yan sanda Kayode Egbetokun ado da sabon mukami a fadar Villa.
Cikakkun bayanai anjima…
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com