Yan bindiga sun sake tafka barna sun kashe jama'a da dama a wata jihar Arewa


Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyukan Sakiddar Magaji da Janbako a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, inda suka kashe mutane goma
.

 Majiyar al’ummar Janbako ta tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Lahadin da ta gabata, inda ta bayyana cewa wasu da dama sun jikkata. PM News ta rahoto.

 Dangane da lamarin na baya-bayan nan, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi Allah wadai da harin da aka kai kan wasu al'ummomi biyu a karamar hukumar Maradun ta jihar.

 Ya kira harin da "na katsalandan da ba gaira ba dalili a kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba," ya kara da cewa gwamnatinsa ba za ta nade hannunta ba sannan ta bari ana aikata muggan laifuka da ta'addanci ba tare da wani sakamako ba.

 Da yake jajantawa iyalan wadanda suka rasu, gwamnan ya kuma jajanta wa wadanda suka jikkata a lamarin, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.

 Hakazalika, dakarun Operation Hadarin Daji sun kashe 'yan ta'adda biyar da suka kai hare-haren al'umma.

 A cewar wata majiya mai karfi a jihar, dakarun da ke sintiri a sansanin ‘Forward Operating Base Bakura’ sun samu sahihin bayanai game da harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Rogoji da ke karamar hukumar Bakura da kuma kauyen Sakiddar Magaji da ke gundumar Janbako a karamar hukumar Maradun ta jihar.

 “Da isar su kauyen, ‘yan fashin sun gudu bayan da suka ga sojoji, a sakamakon haka, sojoji sun ci gaba da bibiyar ‘yan bindigar da mumunar barin wuta kuma a cikin haka, an kashe ‘yan bindiga biyar,” in ji majiyar.

 Sojojin sun kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu, alburusai, shanu da ba a san adadinsu ba, awaki da jakuna da ba a tantance adadinsu ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN