Malam Mousa Ubandawaki mataimakin daraktan yada labarai na hukumar alhazai ta kasa NAHCON ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin Makkah ranar Litinin. PM News ta rahoto.
Ubandawaki ya ce matakin wani bangare ne na kokarin magance matsalar rashin isassun tantuna da aka ware wa alhazan Najeriya a Muna.
Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan korafin da NAHCON ta kai wa Muttawwif na Alhazai na kasashen Larabawa kan rashin isassun tantuna, rashin wadataccen abinci, da kuma karancin abinci ga maniyyatan.
Muttawwif yayin da ya ke ba da hakuri kan yadda aka yi wa mahajjatan Najeriya, ya yi alkawarin mayar da alhazan zuwa sansanin kasar Turkiyya wanda zai iya daukar kimanin mahajjata 10,000 cikin sauki.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com