Tinubu ba zai ci zabe ba da Buhari ya cire tallafin mai - Garba Shehu


Garba Shehu, mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin din da ta gabata ya ce da jam’iyyar APC ta yi asarar shugabancin kasar idan har tsohon shugaban kasar ya cire tallafin man fetur. PM News ta rahoto.

 Shugaban kasa, Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a lokacin, da kyar ne ya lashe zaben shugaban kasa saboda rashin jin dadin gwamnatin Buhari daga jama'a .

 Tinubu ya cire tallafin man fetur nan da nan da ya hau mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, tare da furta a cikin jawabinsa na farko cewa, " tallafin man fetur ya zo karshe."

 Shehu, a wani dogon sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, ya ce:

 “dole ne mu kasance masu gaskiya a siyasance da kanmu.  Gwamnatin Buhari a kwanakinta na karshe ba za ta iya tafiya gaba daya ba domin APC ta yi zaben da za ta ci.  

Kuma da hakan ya kasance ga duk wata jam’iyyar siyasa da ke neman zabe a wani wa’adi tare da sabon shugabanta".


By/Daga - Click/Latsa isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN