An kama wani dan sanda da yunkurin kashe abokin aikinsa a Arewa


Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta cafke wani jami’in dan sanda mai suna Insifekta Moses Paul da laifin yunkurin kashe abokin aikin sa, Insifekta Simnawa Paul, a lokacin da suke bakin aiki a ofishin rundunar ‘yan sanda ta Mobile Force na 62 Squadron Kafanchan a ranar 16 ga watan Yuni.


 Rundunar ‘yan sandan cikin wata sanarwa da ta fitar a yau, 26 ga watan Yuni, ta ce Sufeto Moses Paul ya yi kokarin shake abokin aikinsa, ta hanyar amfani da igiy.  Sanarwar ta ce ''Duk da haka wasu 'yan sanda biyu ne suka ceto abokin aikin saboda kukan da ya yi.''


 Rundunar ‘yan sandan ta kara da cewa binciken farko ya nuna dalilin farko shi ne yunkurin kwace bindigar sufeto Simnawa Paul yayin da za a gano dalilin da ya sa rikici ya barke tsakaninsu tae da daukan mataki a karshen cikakken bincike inda mai laifin zai fuskanci shari’a da hukunci.

By/Daga - Click/Latsa isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN