Sa'o'i kadan bayan dakatar da AbdulRasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, ta gayyace shi domin amsa tambayoyi.
Sanarwar da mai magana da yawun SSS, Peter Afunanya, ya fitar a daren Laraba ta ce Mista Bawa ya isa ofishin ‘yan sandan sirrin ‘yan mintoci kadan da suka gabata. DailyNigerian ya rahotu.
“Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gayyaci Mista Abdulrasheed Bawa, dakataccen shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.
"Bawa ya iso 'yan sa'o'i da suka wuce," in ji sanarwar.
BY isyaku.com