Yadda mahaifar wata mata da ta haihu ya yi batan dabo a wani asibiti

Yadda mahaifar wata mata da ta haihu ya yi batan dabo a wani asibiti

Rundunar ‘yan sanda a jihar Ondo ta kama wata ma’aikaciyar jinya, ma’aikaciyar lafiya da kuma mai gadi a cibiyar lafiya ta Comprehensive Health Centre, da ke garin Emure-IIe, a karamar hukumar Owo, bisa ga wani abin al’ajabi na bacewar mahaifar wani jariri.

 Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Olufunmilayo Odunlami-Omisanya, ya bayyana cewa an kama mutanen uku ne bayan mahaifin jariri mai shekaru 23, Tunde Ijanusi, ya koka kan lamarin a ofishin ‘yan sanda na Emure-Ile. 

Ya ce mahaifiyar mai shayarwa ‘yar shekara 19 ta haifi diya mace a ranar 15 ga watan Yuni a cibiyar lafiya kuma lokacin da mahaifin jaririn ya nemi a ba shi mahaifa, ma’aikaciyar jinya da mataimakinta sun kasa yin bayani inda mahaifar yake. 

 Da yake zantawa da manema labarai, mahaifin jaririn, Ijanusi, ya ce ya damu matuka bayan da ma’aikatan lafiya da suka dauki nauyin haihuwa suka kasa ba su mahaifar jariri kamar yadda aka saba.  

Ita ma da take magana, kakar mahaifin jaririn, Misis Funmilayo Ijanusi, ta ce bayanu da jami’an asibitin suka bayar na cewa wani kare ya shiga cikin dakin ya yi awon gaba da mahaifar ba abin yarda ba ne.  

Ta ce jami’an ma’aikatan cibiyar sun yi kokarin shawo kan ‘yan uwa da su yi hakuri su bar maganar, su kuma asibiti za ta sallami mahaifiyar jaririyar ba tare da an karbi ko sisi ba.

By/Daga - Click/Latsa isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN