Hukumar Kwastam ta Najeriya NCS, reshen jihar Kebbi, ta kama tare da mikawa hukumar NDLEA Kebbi kunshi 104 na surkin tabar wiwi, buhunan diazepam 359 da fakiti 70 na tramadol.
An bayyana hakan ne a yayin mika maganin da Kwanturolan Hukumar Kwastam ta Jihar Kebbi Dakta Ben Oramalugo ga Kwamandan Hukumar NDLEA ta Jihar Kebbi a hedikwatar Hukumar Kwastam a Birnin kebbi a ranar Juma’a 16 ga watan Yuni, 2023.
Oramalugo ya ce jami’an rundunar sun samu nasarar cafke wata mota ta tsayawa da bincike a kan hanyar Kamba/Kyangakwai biyo bayan samun bayanai.
Ya kara da cewa jami’an hukumar sun iya gano motar da ta dace da wanda ake zargin tana dauke da kwawoyin.
“Bayan cikakken bincike da nazari kan motar da aka ambata ta yi daidai da bayanin motar da ake zargi da chasis No. IHGRC3KEA246069 kuma an yi sa’a, an kama ta dauke da fakiti É—ari da huÉ—u (104) ( girman kwamfutar tafi-da-gidanka 1kg kowace) na tabar wiwi, da casa'in tara (99) An gano kwayoyin diazepam 5mg a boye a cikin motar wanda ake zargin mai suna Suleiman Yusuf (wanda aka fi sani da Babangida) ya tuka."
“A wani lamari makamancin haka, an kama wasu kwayoyi da aka yi watsi da su na fakiti 70 na TramakingTtramadol (225mg) da diazepam tablets (5mg) 260 a ranar Litinin, 5 ga Yuni, 2023 a dajin Kamba/Rijiyar Maikafi ta hannun jami’an sintiri na kwastam, amma babu wanda aka an kama". Ya kara da cewa.
Dokta Oramalugo ya ce darajar kudin haraji na kayan da aka kama ya kai miliyan talatin da bakwai, dubu dari takwas da ashirin (N37, 820,000) kuma wanda ake zargin za a mika shi ga hukumar NDLEA ta jihar Kebbi domin ci gaba da daukar mataki.
A cewar Kwanturolan NCS, abubuwan da aka kama a cikin lokacin da ake bitar su sune:
1. Surki 104 na tabar wiwi da alliran diazepam 99 (5mg)
2. fakiti 70 na Tramaking/Tramadol (225mg) da diazepam 260 (5mg)
3. shinkafa 107 na kasa waje (50kg)
4. Dila 38 na kayan gwanjo
5. 1.275 lita na PMS man fetur
6. Jarka 52 na mangyada
7. Mota 1 Honda Accord 2014
8. Mota 1 kirar opel da aka yi amfani da ita
“Kimar kudin haraji (DPV) na kayayyakin ya kai miliyan sittin da hudu da dari shida da dubu goma sha uku da dari biyar da casa’in da hudu (N64, 613, 594)”. Yace.
Dokta Oramalugo ya yabawa zaratan jami'an hukumar bisa jajircewarsu da kishin kasa wajen tabbatar da nasarar aikin. Ya kara da cewa rundunar za ta yi tsayin daka wajen gudanar da aikinta tare da tsayawa kan dakile harkar fasa-kwauri, musamman man fetur da kuma shinkafar da aka dauko daga kasashen waje.
BY isyaku.com