Dakataccen shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, na ci gaba da kasancewa a tsare a hannun rundunar ƴan sandan farin kaya, sati ɗaya bayan cafke shi, Daily Trust ta rahoto.
Duk da cewa jami'an hukumar basu bayyana laifukan da ake tuhumarsa da su ba, an fahimci cewa ana ci gaba da yi wa Bawa tambayoyi ne bisa rawar da ya taka wajen sauya fasalin kuÉ—i.
Wani majiya ya bayyana cewa akwai sauran wasu abubuwan da ake tatsar bayanai daga wajensa a kansu, amma dai rawar da ya taka a wajen sauya fasalin kuÉ—in ita ce akan gaba.
Jami'an rundunar ta DSS dai sun yi caraf da Bawa ne jim kaɗan bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shi. Legit ya wallafa.
Ana ta kiraye-kirayen a saki Bawa
A halin da ake ciki ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun bayyana kuskuren DSS na ci gaba da tsare shi, inda suka yi kiran da ko dai a maka shi kotu ko kuma a sake shi ya shaƙi iskar ƴanci.
Wani ɗan rajin kare haƙƙin ɗan adam mai suna Salihu Aliyu, ya bayyana cewa:
"Yakamata DSS ta gaggauta bincikenta kan waÉ—annan mutanen, ina nufin Bawa da Godwin Emefiele, musamman na EFCC (Bawa) sannan ta tura su zuwa kotu. Ba mu san wane irin laifi ma ya aikata ba har yanzu!"
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar DSS, Peter Afunanya, ya ci tura saboda ƙin ɗaga wayarsa da ya yi. Bai kuma dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba a wayarsa har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
DSS Ta Dira Gidan Abdulrasheed Bawa
Rahoto ya zo cewa rundunar Æ´an sandan farin kaya ta da DSS na ci gaba da zurfafa binciken da ta ke yi akan dakataccen shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa.
Jami'an rundunar sun dira gidan Bawa domin samo wasu hujjoji kan binciken da su ke yi a kansa.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com